A Bond Broken 1
Waya ke ringing da vibrating at the same time. Agogon bango ya nuna karfe shida saura kwata na asuba. Sound din sai ya zama muffled sakamakon tana cikin quilt a nannade. Mai ita bai dauka ba har ta katse aka sake kira. Yayi siririn tsaki irin na wanda bacci bai ishe shi ba ya mika hannu kenan da niyar kashe alarm sai ya tuna ringtone dinsa ne fa ba sound din alarm ba. Da sauri ya wartsake ya kama neman wayar amma tayi nisa. Garin neman nata ya sake nade kansa cikin quilt din ya kuma hargitsa gadon. He got tired and stood up ya bude quilt din yayi shaking ɗinsa. Hakan yasa wayar ta fada kasa tayi karkashin gado. Ya kwanta ya zura hannu zai daukota sai shi da quilt din nasa suka fado kasa with a thud.
“Auchhh” ya dafe gefen gaban kansa da hannu daya. Da dayan kuma yana kwance a kasan ya kara wayar a kunnensa bayan yaga sunan mai kiran “you do know that I abhor early morning calls right?”
“Abeg save me from your grammar da safiyar nan.” A lady answered from the other side.
Her ever jovial tone wanda ke nufin all is well ne yasa shi samun nutsuwar cewa “You better have a tangible reason for calling Twinnie, if not Allah sai nayi miki rashin M. I was having one of the best dreams of my life. An yi min alkawarin blank cheque naje karba wayarki ta tashe ni. Yar bakinciki kawai.”
Dariya tayi “Allah Ya raba ka da son kudi Twinnie.”
“Ba amin ba. Muna son halal, za kuma mu cigaba da nema.” Ya kaurara muryarsa “why did you call?”
“Can you please come over and drive the kids to school? Yau da ciwon kafa na tashi.”
Hamdaan knows better than to start complaining about her request. Hamida is heavily pregnant with her third child. Mijinta ba mazauni bane. Always travelling around the country and overseas sometimes.
“Gani nan in sha Allah.” Was his answer as he got up to start getting ready.
Hamida smiled as she turned to her worried looking husband.
“Ka karasa shirin ka zai zo.”
He let out a deep breathe and thanked her. Tafiya ce ta kama shi yau babu shiri. After eleven na dare yayi recieving call wanda ya bata masa plan dinsa na yin two weeks a gida. He has to be at the airport by eight to fly to Lagos. Unfortunately for them two days kenan da driver dinsu ya yi tafiya. Sun kwana da niyyar Hamida za ta kai yaran school sai ta tashi da ciwon kafa irin na masu cikin da ya soma nauyi. Shi ne dalilin kiran da ta yiwa twin brother dinta.
Hamdaan was at the house a few minutes to seven all dressed for the cold weather. Blue faded jeans, long sleeve shirt and a hoodie. His handsome face covered in his helmet. The kids Amal and Hanan were very excited da ya shiga gidan. He is that playful Uncle da idan ya shiga cikin yara sai addu’a kawai. He plays too much; all three of his sisters keep saying.
His response was always “life is too serious. Man needs to create distractions.”
Yaran suna breakfast Tahir mijin Hamida ya fito a shirye. He was dressed in a sage coloured tweed suit da grey designer cover shoes which match his tie. Yana rike da briefcase ita kuma Hamida tana jan trolley bag dinsa. Hamdaan yana ganinsu ya tashi ya janye trolley din. A wajensa wannan ma aikin wahala ne, ita da take ciwon kafa she was supposed to be in bed.
“Allah Ya baka hakuri nima nace ta kawo tun a ciki ta ki.” Tahir said with a smile. Yafi kowa sanin Hamdaan is an over protective brother or rather twin.
To a hakan ma bai tsira ba, Hamdaan cewa yayi “Da sai ka zare mata ido don ta hakura. Yawan tafiyar zai iya hana ciwon kafar warkewa da wuri.”
He never realy liked Tahir. Ya taba fadawa Ummansu wai yana da wani vibe da yake rubbing dinsa in a certain way he dislikes.
Sun gaisa ba yabo babu fallasa Hamdaan ya zauna jiran yaran su gama cin abinci. Hamida kuma tana ta fama da Tahir akan ko tea ya sha amma ya ce yana gudun missing flight. Musamman da abokin tafiyarsa yake ta kiransa. He left shortly bayan ya yi sallama da yaransa.
“Ya Rabb, Twinnie don Allah duba idan Daddyn Amal bai yi nisa ba.”
“Sai in yi masa me?” Ya bata amsa yana danna waya.
“File din nan ya bari. Tun dare ya hada takardun yace da su zai yi presentation anjima.”
“Zai dawo fa idan ya kula ya barsu.” Hamdaan answered with a very nonchalant shrug.
“Hamdaan please” Hamida ta danne bacin ran da ya soma taso mata saboda yadda yake yi.
“Don Allah ki bari ko scanning sai kiyi masa. Na tabbata yanzu ya bar unguwar nan. Kuma idan na bi shi su Hanan za su makara.”
“Let me worry about them. Ka tashi ka bi shi.” Tayi magana tana ta kiran wayarsa amma yana wata wayar.
Gyara zama yayi abinsa sai gani yayi ta dauki car keys da hijab za ta fita. Bai san lokacin da ya tashi da sauri ba ya karbe file din daga hannunta. Su ka kalli juna kowa ransa a bace. Kamaninsu a lokacin ya kara bayyana sosai. Ko magana bai yi mata ba ya fita.
Bike dinsa ya hau don zai fi masa sauki. Titi daya ne na fita daga unguwar. Ya kama hanya da niyyar zuwa airport din idan basu hadu ba a hanya. Tafiyar less than five minutes ya hango motar Tahir. Ya kama binsa a baya sai dai to his surprise titin da yake kai ba na zuwa airport bane. Yana cikin mamaki Hamida ta kira shi. He answered her da airpod din kunnensa ya ce mata ya hango motar.
“Yauwa kayi sauri. Ina ta kiransa amma waya yake yi.”
“Kuma ya kasa katsewa ya saurare ki?”
“Allah Ya shirye ka.” Kawai ta ce ta katse kiran.
Hamdaan continued to follow Tahir har zuwa wata unguwar daban. Shi dai ya san indai jirgin karfe takwas ne to tabbas wanda yake wajen nan a yanzu dole yayi missing dinsa. A bakin gate din wani gida yaga Tahir yayi parking. Shi kuwa sai ya tsaya nesa kadan dashi don kada ya hango shi. Yana hango Tahir din ya fita ya shiga gidan. Bayan kamar minti goma su ka fito da wasu mata guda hudu. Babba dattijuwa sai yan mata biyu, daya tana jan akwati karami shi kuma Tahir yana jan babban. Ta hudun kuwa ciki gareta yayi girma sosai. Hamdaan could hear his heart pounding saboda tsananin fargabar da ya shiga. Yana kallo aka saka akwatunan a booth.
The elderly woman waved at the pregnant one ta koma ciki tare da daya daga cikin yan matan. Wadda ta rage ta shiga baya. Ita kuma mai cikin Tahir ya taimaka mata ta shiga gaba. The way he held her was just too cosy.
It took Hamdaan some minutes to realise tsayuwar banza yake yi. He quickly turned on his bike ya bisu a baya har airport. He patiently waited har jirginsu ya tashi karfe tara daidai sannan ya tambayi wani ma’aikaci a wajen flight din ina zai je.
“Abuja” Was the quick answer.
His heart sank deeper in his chest. He felt hot duk da ba zazzabi bane a jikinsa. With shaky hands ya bude file din da Hamida ta bashi. Inside were papers…letter headed papers of his company containing random unrelated headlines all dated months back. Hannunsa ya dunkule ya dora akan bakinsa to prevent himself from lashing out a gaban mutane.
To be continued…
Drop your thoughts.
Ooops! Join The Community To View The Comments