A Bond Broken 2
Disappointment was written in bold letters a fuskar Hamida da Hamdaan ya koma da file din nan.
“Kai ma baka same shi a wayar ba ko?” Ta ce cikin damuwa.
“Uhmm.”
Tausayinta yake ji sosai. Sannan abin da ya gani ya tsaya masa a wuya tamkar kayar kifi. He is trying to control his temper shi yasa yaki yin doguwar magana da ita. He cannot bring himself to tell her what he saw. Atleast ya kamata ya san wacece matar da alakarsu da Tahir kafin ya tayar mata da hankali. A half baked story a halin da take ciki is not good musamman ga mace irinta mai saka abu a rai.
“Ni zan wuce gida ko akwai abin da kike bukata?”
“A’a, nagode.”
She looked worried sick kamar yadda kowacce ideal wife ya kamata taji. Normal miji nagari wanda ya cancanci matarsa ta shiga damuwa akan lamarinsa would have been elated. Shi kan shi Hamdaan din da bai ga wannan abu ba zai ji komai ba. Daidai ne mace ta damu da duk abin da ta san zai janyowa mijinta matsala.
Kasa fita yayi ya tsaya a bakin kofa ya kalle ta “Mene ne kuma Hamida? Naga duk kin yi wani iri.”
Kamar jira take ace kule, yana rufe bakinsa ta fashe masa da kuka. It was coming deep down from her heart. Har tsoro ta bashi yadda take hadiyar zuciya. Allah Yasa Amal da Hanan suna can dakinsu suna wasan guje-gujen murnar yau basu je school ba.
“Wani abin ne kuma ya faru bayan na fita?” Ya tambayeta bayan ya dawo ciki ya zauna suna fuskantar juna.
“Ban san yaya zai yi ba. He spent the night yana harhada takardun nan. Gashi Ogansa masifaffe ne…” ta kare maganar helplessly. Sai kuma ta kalle shi wit a bit of hope “ko in sanar da Abba ya kira Baba Musa a yiwa Ogan nasa magana?”
Allah ne Ya kiyaye amma tabbas Hamdaan ya kusa taya yar uwarsa kuka saboda yanayin da ya tsinci kansa. Tahir will be damned idan ya kasance macuci. Ji yadda ta fita hayyacinta kamar wadda aka yiwa duka. He decided to let her get a glimpse of her husband. Wayarta ya dora mata a tafin hannu.
“Ki bi takardun one by one kiyi scanning sai ki tura masa mana. He can download and print a can. It’s no big deal Twinnie.”
Ba kunya ta share hawayenta harda kai masa duka wai me ya hana shi fada mata tun da wuri.
“Abin da na fara fada miki kenan kafin na fita. Amma saboda kina dadi miji ko saurarona baki yi ba.”
Kunya taji ga wani uban murmushi kamar anyi mata albishir da kujerar Makka. Ya girgiza kai shima yana murmushi don kada ta zargi komai. Bai jima ba yayi mata sallama ya tafi gida.
Hamida aiki ya samu. Takardun cikin file din ta fitar a jere yadda suke don ma kada tayi mistake. Ta dora camera akan ta farko za ta dauka kenan ta kula da kwanan watan dake rubuce a kasan takardar a tsakiyar stamp din da aka yi mata. A hankali ta ajiyeta ta dauko ta bayanta. Ita kam ta 2020 ce ma, shekara hudu da suka wuce tun ana lockdown. Ai bata san lokacin da ta wargaza takardun ba lokaci guda tana duddubawa.
Abin ya daure mata kai matuka. Ta ajiye file din da sanyin jiki. Yanzu akan wannan ta wahalar da Hamdaan? Tunaninta sam bai tafi kan me yasa Tahir ya bar wannan file din ba. Ta yarda dashi. Kanta ta dorawa laifin dauko wrong file da zaton shi ne wanda zai tafi dashi.
Bata yi kasa a gwiwa ba ta kira Hamdaan ta fada masa sannan ta bashi hakuri.
“Maybe ban kula da kyau bane.”
“No worries” ya ce mata a ransa yana mamakin yadda tayi convincing kanta cewa ita ce bata kula ba.
*
“Mama wallahi jikin da sauki fa. Kinga ma tuwo na gama kwashewa zan shiga wanka.”
Ramat ta juya wayarta ta nuna dinning table tana nuna abubuwan da suke kai.
Banda tuwon shinkafa da miyar taushe, tayi fruit salad da kunun aya saboda shi Tahir yake sha’awar sha.
She could sense rashin jindadin aikin da tayi daga mamanta saboda bata sami yabon kokarinta da tayi tunanin samu ba.
“Allah Mama da sauki sosai.” Ta sake fada with a big smile.
“Kin dai san wahalar da aka sha kafin cikin nan ya zauna.” Sai kuma ta kama fada “Me Inaya take yi da ba za tayi miki tuwon ba? Ba don ta taimaka miki na turo ta ba?”
Ramat didn’t know how to explain to Mama cewa Tahir baya son abincin kowa idan tana kusa.
“Sha’awar girkin nayi.”
“Sha’awa ko? Har kin manta koke-koken da kika dinga yi da jini ya balle miki kwanaki? Idan ba kya bukatarta gobe a kaita tasha ta dawo gida.” Ta katse kiran bayan taja tsaki.
Ramat only smiled. Mama is looking out for her tafi kowa sanin haka. Matsalarta guda, ita ce yadda Maman ta kan yi wasu abubuwa kamar ta manta aure gareta yanzu. Ko hamma tayi sai Mama ta ce hala Tahir ne ya hadata da aikin da ya hanata bacci. Yanzu ma albarkacin cikin nan ne abubuwa suka ragu. Tsangwamar da take yiwa Tahir din ta ja baya tunda ga zuri’a za a fara hadawa.
*
A daki sanye da bubu irin ta shan iskar nan da hula budurwa ce da bata fi twenty three years ba. Aikin goge-gogen lungu da sakon dakin take yi saboda kurar da ta hadu a kwanakin da suka yi a Kano. Everywhere is sparkling but it seems she is just getting started. Bata son barin kura ko kadan saboda Ramat is asthmatic. Kowa yana tattalin abin da yake cikinta, ita kuwa tafi damuwa da lafiyar yar uwarta. She is being extra cautious don samun attack a yanayin da take ciki yanzu will not be funny. Shi ne tun dawowarsu daga Kano dazu take ta faman gyaran gida.
Tausayinta take ji saboda ba ƙaramar wahala cikin yake bata ba . After all the IVF procedures, da aka samu nasara ya zo mata da laulayin gaske. Kwanciyarta a asibiti har an daina kirgawa. Da ta taba samun attack babu wani masoyinta na kusa da bai zubar da hawaye ba. Shi ne dalilin da yasa mamansu ta turota ta zauna har haihuwa. Being her only sister saboda gidansu duk maza ne, she took a whole semester leave ta dawo Abuja daga Minna.
Tana aikin taji waya na ringing amma sound din baya fita sosai. Throw pillows din kujerar da cushion ta dinga dagawa har tayi sa’ar ganin wayar. Ta duba sunan mai kiran an saka (Mi Love). She squintted her eyes in wonder. Tun zuwanta gidan bata taba ganin wayar ba. Mai kiran kuma is not relenting. Yana katsewa ake calling back immediately.
“Anti Ramat ana waya.”
Ta dauki wayar ta fito falo. Ramat tana jin ringtone din ta taho da wani irin sauri da bai kamata a gani a wajen wadda tayi nauyi kamarta ba. Tana zuwa ta karbe wayar. Actually fizga ma tayi.
“Inaya kin daga ne?”
The young lady looked at her suspiciously. And because she is not someone who likes beating around the bush sai ta rage muryarta.
“Anti Ramat affiar? Saurayi gareki? Mun shiga uku.”
“Amma baki da mutumci Inaya. Ni ce mai saurayin?”
“Naga sai muzurai kike yi ne.” Inaya replied da dan murmushi.
Ramat ta harare ta
“Kuma baki yi tunanin ko numbar Tahir bace nayi saving a haka ba?”
“You look like a criminal. And…” Inaya ta nuna wayar “ba taki bace saboda ba sabuwa bace.”
Ramat ta dade da daina mamakin sharpness din kanwarta. Mutum ce mai lura sosai. She just have to salvage the situation kafin Inaya ta saka ta a tight corner.
“Wayar Tahir ce.”
“Oh…Ohk”
And she just continued her work. Ramat ta kasa gane manufar amsarta. Ta yarda ne ko kuwa? She kept trying to lock eyes with her amma sam Inaya taki yarda hakan ta faru. Hankalinta yana kan jikin wardrobe da ta kama gogewa ba ji ba gani.
Sai da Ramat din ta fita ta kalli kofar dakin tana girgiza kai. She sat down and took a deep breath. At her age gani take ta gama sanin halin maza ciki da waje. Mijin yayarta was a saint and more lokacin da suna courtship har aka yi auren. Har fatan samun miji mai rabin halinsa ta dinga yi. Kuma a shekara hudun da suka yi auren still mutumcinsa take gani.
Zuciyarta tana raya mata akwai wani abu da suke boyewa ne bayan zuwanta gidan. Ramat is too damn cautious around her. Su da tazarar shekaru bai taba hanasu zama free da juna ba. Sai gashi yanzu komai kaffa-kaffa suke yi ita da Tahir kamar suna boyon wani abu. Inaya knows something is amiss. Tana son sanin inda matsalar take, but she does not want to pry. She just sighed and continued with her work.
- •••••••••••••••••••••••••••••
A kwana guda da Hamdaan yayi yana tunanin best way to tackle matsalar Tahir har wani fadawa yayi. Idanunsa zuru-zuru da ya tashi da safe. He had less than 3 hours sleep throughout the night. Every part of his being is telling him kada yayi brushing abin da ya gani aside. So a thought crossed his mind. Da yamma kuwa a ranar ya shirya cikin manyan kaya ya dauki mota ya fita. Bai tsaya ko ina ba sai gidan da Tahir ya dauki matan nan jiya.
Jikin motarsa ya koma ya jingina bayan ya tura yarinyar da ta fito ganin waye da ya kwankwasa karamin gate din gidan. Few minutes later wani dattijo ya fito. Ya bawa Hamdaan hannu suka gaisa cikin mutuntawa.
“Ban gane ka ba dan saurayi.” Dattijon ya fadi yana murmushi.
“Haka ne Baba.” Fadin sunansa na gaskiya ba dabara bace shi yasa ya ce “Suna na Hassan Alhassan.” Sannan ya dukar da kai ya kwatanta fitowar Tahir da matan nan.
“Dama wadda suka tafi tare ce….uhmm…” ya kama susar keya.
Dattijon ya fadada murmushinsa “wata mai dan jiki ko?”
Hamdaan ya gyada kai yace eh, bayan ko da wuka a wuyansa he cannot make out any of the ladies except the pregnant one. Ita ce ya karewa kallo tunda yaga irin rikon da Tahir yayi mata.
“Ganin da kayi musu jiyan komawa gida zasu yi. Bakin iyalina ne.”
Hamdaan felt a heavy jolt of disappointment and uttered “Subhanallah” silently.
“Kada ka sami damuwa. Jirani ina zuwa.”
Bawan Allah ya koma ciki ya kira yarsa wadda aka raka matan bakin mota da ita yasa ta rubuta masa nambar wayarta. Bakin nasu satinsu daya amma sabo ya shiga tsakanin yarsa da yar budurwar da ta zo da yayarsa, su ka yi exchanging numbers.
Waje ya dawo ya mikawa Hamdaan “to Mal. Hassan, aji tsoron Allah. Idan ka san ba da kyakkyawar niyya kake nemanta ba kada ka kira don Allah. Kamar yadda nace bakuwa ce yarinyar. Mutumci da nake hasashe a tare da kai ne yasa ni karbo maka lambarta.”
Feeling a bit guilty, Hamdaan thanked the man profusely sannan ya dan sosa keya ya ce
“Don Allah Baba yaya sunanta?”
“Inaya. Inaya sunanta.”
Ohhky…me kuke tunanin zai faru a gaba???
Ooops! Join The Community To View The Comments