A Bond Broken 3
Alh. Hassan Ali (Abba) is a household name in Kano. Asalinsa mutumin Gombe ne daga karamar hukumar Funakaye. Karatu ne ya fito dashi daga garinsu cikin sa’a kuma ya kafa kasuwancin da ake damawa dashi. Kamfanin robobi gare shi wanda ya bunkasa har suke hadawa da su detergent, biscuit da drinks. Matarsa ɗaya Salma (Mami) mutuniyar Katsina. Ita da ƴan uwanta duka a Kano aka haife su. Nasu gidan na ƴan boko ne tuƙuru. Associate Professor ce a Kano State University yanzu. Ƴaƴansu biyar, Maryam, Amira, Kulsum sai ƴan biyu Hamida da Hamdaan.
Two contrasting personalities ne suka haɗu a matsayin iyayen gidan. Ɗan kasuwa da ƴar boko. As they say, unlike forces attract. The kind of love shared between Abba and Mami is wholesome with a little bit of playful fights to spice it up. Yaran are always caught a tsakani. Da suka girma kullum suna cikin canja favourite. Inda suka ga interest ɗinsu yafi ƙarfi suke zuwa. Hamdaan ne kaɗai Mami’s boy. Petting ɗinsa take yi sosai saboda shi ne auta tunda Hamida ta fara haifa. Idan tsokanarsa ta tashi ne dai har ita baya ƙyalewa.
*
Da Hamdaan ya dawo gida ɗakin Mami ya tafi. A buɗe ƙofar take. Ya hangota tana kwalliya kamar yadda ta saba. Yayi sallama ta amsa ta juyo da turare a hannu.
Ƴar ƙarama ce Mami. Babu tsayi babu ƙiba. Duka ƴaƴanta sun fita girma. Jikin Abba suka biyo. Yana da tsaho kuma da girma yazo yayi jiki da tumbi.
Hamdaan ya shiga ɗakin yana zolayarta
“Haj. Mami yau Abba zai dawo ne?”
Ta harare shi
“Ɗan ƙaniya ka raina ni fa. Wato ba na ado sai tsohonka zai dawo.”
“Maminmu kenan. Wai ɗan ƙaniya. To yanzu kalmar nan masculine ce ko feminine? Wai don na san da wa kike a cikin iyayen nawa.”
Dariya ce ta ƙwace masa saboda biyo shi da tayi da kwalbar turaren da bata samu ta fesa ba. Ya juya a guje bata haƙura ba ta cigaba da binsa.
Ya dinga dariya.
“Mami ki bar gudu. Jefe ni kawai da turaren ki hutar da kan ki.”
“Wato asara ta hau ni, to naƙi ɗin. Kuma ka tsaya nan in buge ka wallahi don na gaji.” Ta jingina da bango, hannunta a ƙirji.
Hakin da yaga tana yi sai ya tsaya ya dawo gabanta ya rage tsayi.
“Mami zafin hannu ne dake fa. Abba ba zai ji daɗi ba idan ya san baki ji maganarsa kin daina dukana ba.”
A kafaɗarsa ta ɗora hannunta ya kaita kujera ta zauna.
“Ka samo mata ka gani in zan sake dukan ka mana.”
Remembering the number he got, he decided to brighten her mood.
“Na gano wata…”
Mami ta gyara zama.
Hamdaan yayi murmushi “bata sanni ba tukunna. Yau na samo number ɗinta.”
She smiled “Allah Yasa abokiyar zaman ce ka gano Hamdaan. It’s high time you settle down too.”
Hamdaan ko a zuci bai ce Amin ba. Yarinyar da bata da bambanci da gaibu saboda rashin saninta yaushe zai amsa addu’ar baki mai tsada irin na Mami a kanta? Sallamar Abba suka ji. Nan take murmushin Mami ya ƙara faɗi. Ta tashi ta tarbo shi a bakin ƙofa. Ya zuba mata idanu yana jindaɗi.
“Ansalmemen Hassan.” Ya kirata da sunan da kunnuwanta kaɗai ke ji.
Hannu ta saka tana patting lips ɗinta alamun yayi shiru.
“Hamdaan. Idan yaji sunan nan sai yayi min handsfree wajen yayyensa.”
Abba yayi dariya yana nuna mata bayanta.
“Yaron naki ai ya san me yake yi. Kina tasowa ya gudu. Suna kuma tun yaushe suka sani. They just know better than to start saying it out loud.”
Ta juya kuwa Hamdaan babu shi babu dalilinsa. Abin dariya ma ya bata. Ta karɓi briefcase ɗin Abba suka tafi part ɗinsa.
Bayan Hamdaan yayi wanka, wayarsa ya ɗauko yana duba sunan da yayi saving na Inaya. Ya so kira a lokacin amma bai san me zai ce ba. Yaje mata a matsayin masoyin da yayi ƙarya ne ko kuwa kawai ya tambayeta alaƙarsu da Tahir?
***
Few days later, daga kitchen Hamida taji wayarta tana ringing a falo. Kafin ta fito har Amal ta ɗauka ta soma surutu.
“Daddy kaga Hanan ta yaga min story book ɗina ko?”
Fiercely Amal ta ce “Daddy ƙarya take yi. A yage yake.”
“Daddy ita ce” Amal ta kuma faɗa. Da yake kuma tafi ƙanwarta raunin zuciya sai ta kama kuka.
Hanan ma kukan ta fara “Allah Daddy bani ba ce. Ban ɗaukar mata ba.”
From his side Tahir ya rikice ya rasa wa zai fara bawa haƙuri.
“A bawa Mummy wayar. Idan na dawo zan kawo sabon story book.”
“Daddy ni fa?” Said Hanan.
“Ke da baki iya karatu ba” Amal ta murguɗa mata baki.
Da ƙyar Hamida ta karɓe wayarta tana bashi haƙuri.
“How is my Babe and baby? Ƙafar ta daina kumburin?”
“Much better Hon. Sai missing tausar nan da kake yi musu.” Idanunta akan yatsun ƙafar take magana.
“Tausa dai na koyawa Amal saboda irin wannan lokacin. Ki kirata tayi miki indai ba kuma wani abin kike nema ba” he ended teasingly.
Hamida pouted her lips kamar yana gabanta.
“Laifi ne idan nayi missing ɗin ka Hon?”
Tahir ya ce “Ko kusa. I’ll be home before you know it.”
“Da wannan aikin naku da ba a hutawa? Ban sa rai ba ma.”
He took his time ya dinga bata baki don kada ta damu. Yana nuna mata illar damuwa ga mai ciki. Kafin su gama hirar sai gashi tana dariya sosai. Cikin dabara ya sako mata tambayar dake cin ransa tun ranar da tayi maganar.
“Uhmmm, wai ranar da na tafi da kika bawa Hamdaan file ɗina zuwa ƙofar gida ya biyoni ne?”
“Ina fa! Har airport ya bika. Wayar da kayi tayi ce ta hana mu samunka. Amma yace daga gidan nan har airport yana ganin ka.”
Wani abu mai ɗaci ya taso daga cikin Tahir zuwa bakinsa. Tsoron jin wannan amsar ne ya hana shi matsawa da tambayar tun farko. His hands began to shake. Just how far did Hamdaan follow him? Ƙarya yayi wa Hamida ko kuwa ya bishi ɗin? Why isn’t she saying anything idan haka ne?
“Zan kira shi na ƙara bashi haƙurin wannan wahala da muka saka shi.”
Hamida taji daɗi “no need Hon. Tun a ranar ya haƙura.”
“Nooo. That was his twin. Yanzu kuma mijin twin ne zai yi nashi. Na san ya wahala saboda har sharaɗa na biya.”
Yadda ta ce “Sharaɗa kuma?” Ya nuna masa hankalinta ya tashi.
Ya fara da sanar da ita cewa ai duka wayar da wani colleague ɗinsa yake yi yana yi masa kwatance. A hanya yaji labarin an canja lokacin tashin jirgin. Shi ne abokin aikin ya roƙe shi da ya taimaka ya ɗauko matar maƙocinsa da ƙanwarta?
Hamida tried her best to stay composed amma duk da haka muryarta sounded pissed.
“Matar wa? Hon ban gane wannan alaƙar ba?”
“Maƙocinsa ne a Abuja” ya fara inda-inda.
Angrily Hamida ta cigaba da magana “Abuja ko Lagos?”
“Naga kin tayar da hankali ne. Kinsa na manta me nake cewa. Maƙocinsa a Lagos.” Ya gyara zancen da sauri.
“Are you an errand boy? Fisabilillah Hon ta yaya zai aike ka ɗauko family ɗin maƙocinsa?”
Calmly Tahir ya soma yi mata bayani cewa matar ciki ne da ita tsoho. She just lost her Dad she ne dalilin tahowarta Kano. To top it all shi maƙocin is not well to do. A mota suka zo Kanon. Yanzu da za ta koma cikin ya ƙara tsufa. Abokin aikin nasa out of goodwill ya biya musu kuɗin jirgi ita da ƙanwarta da zata bita ta tayata zaman jego.
“A nan ɗin ma gidansu masu ƙaramin ƙarfi ne. Babe da kin ganta sai kin tausaya mata. She looked malnourished. Shiga mota ma sai da na kama ta saboda har wani jiri take yi”
“Ya Rabb, Hon am sorry. Allah Ya baka lada. I hope ka taimaka musu da kuɗi…” tayi dariya “I trust you will ma.”
“Zama dake ne Babe. Duk wanda yake tare dake dole ya san mahimmancin sadaka. I love you Hamida.”
“Tosh, tosh, toshhhh…kaina ya fashe.” Tayi magana bakinta har kunne.
Tahir kuwa dariya ya dinga yi mata har suka gama wayar. Ta sami waje ta zauna tana murmushi ita kaɗai. She never knew one can fall in love again and again sai a kan mijinta. A duniyarta, bata jin akwai wanda yayi sa’ar abokin rayuwa kamarta. Idan ƙawayenta ko ƴan uwa suna ƙorafi akan how unromantic their spouses are, she only smiles and blush. Tahir is an entirely different breed. Thoughtful and considerate. He is a dream come true!
*
“Hahhhh… that was pretty easy.”
Tahir laughed so hard. Shi kaɗai ne zaune a mota bayan an tashi daga aiki, ya tsaya ya kirata kafin ya tafi gida. Rashin sanin yadda zai kuɓutar da kanta ba tare da ta zarge shi da komai ba ne ya hana shi tambayarta tun farko. Ya jira ko zai ji wani abu ta ɓangarenta amma bata ce komai ba. Does that mean Hamdaan ƙarya yayi mata bai bishi ba kamar yadda tace? Ko kuwa ya bishi ɗin yana jiran ya ɗana masa tarko?
Tunda ya sami kan Hamida, ya tabbatar komai zai zo da sauƙi. He left no stone unturned as always. Ya faɗi gaskiyar komai da yake jin Hamdaan ya gani except tafiyarsa Abuja maimakon Lagos. A yadda ya san bata iya ɓoyewa Hamdaan komai, yana tunanin by now ta riga ta kira shi ta fara yi masa bayani. Duk da haka he dialled his number. Zarginsa kuma ya tabbata. He was on another call!
He laughed again yana tunanin ta rage masa aiki. Ya tayar da motarsa ya bar wajen.
***
“Hamdaan an shiga layin mayaudara, Allah Ya yafe maka.”
Shi ne abin da ya faɗawa kansa a gaban mirror kafin yayi calling ɗin Inaya.
“Salam alaikum.”
Yaji ance daga daya bangaren. It was a soft voice, a very soft one that washed over him from head to toe. Instictively his grip on the phone tightened.
“Wow! Your voice is musical” He blurted out.
“Hmmm” was the reply and “wannan lines ɗin sun tsufa.”
Not surprised at all Hamdaan ya ce “An saba faɗa miki ko?”
“Uhmm” ta amsa a gajarce tana wani jan hamma.
Hamdaan yayi kamar bai gane ba
“I hate to say this amma duka ba ƙarya suka yi miki ba. Allah Yasa ni ne na karshen faɗa dai.”
“Wai wa kake nema ne?” She sounded exasperated. Kana ji ka san dole yasa ta amsa wayar.
He smiled a bit. Ya gama ganota. So take ta bashi haushi ta gudu. Shi kuwa bai shirya hakan ba har sai ya sami hanyar shigo da zancen Tahir yaji amsar da yazo nema.
Da yanayin rashin damuwa ya amsa mata da cewa “Yadda kike amsa min da guntu-guntun wulakancin nan na san kin fahimci wurinki na zo da abin da ya kawo ni.”
Da a gabansa take da yaga yadda ta bude baki da tsananin mamaki. Waye zai zo neman soyayya yace ana amsa masa da guntu-guntun wulakanci?
“Tunda ka gane hakan me ya zaunar da kai?”
Da wani low tone that cought her off guard ya yi mata tambaya.
“Ni ne baki son bawa chance ko kuwa kina da wanda kike so? I’ll back off either ways”
Shiru tayi na dan lokaci tana kara mamakin bluntness dinsa da yar kunyar nata kalaman.
“Me ya kawo ka don Allah? Indai maganar aure ce bani da niyyar yi nan kusa.”
“Wani mugun ya kwafsa mana kenan? Anyi breaking zuciya mai tsada za a janyo min. To Allah Ya isa.”
Despite her initial reservation, Hamdaan heard Inaya’s short genuine laughter in his ears. Wani banzan murmushi ya subuce masa. Da gaske muryarta za ta kashe mutum.
Dama ta samu, ya fara breaking ice din shi yasa ya cigaba. Yana magana abin tausayi dashi ya ce
“Yanzu yaya zaki yi dani? Wuni nayi ina tsara kalaman da zan tashi kan ki dasu. Gashi kuma kin ce baki da niyyar aure.”
Inaya sat down and took a deep breath. Soyayya is realy the last thing on her mind now.
Hamdaan gajiya yayi da shirun ya dan yi gyaran murya “Hey, you there?”
“Ina jin ka.”
Wankin hula na neman kai shi dare daga son yiwa Hamida abin arziki.
“Inaya”
“Ina jin ka nace.”
“All men are the same and different at the same time. Atleast I know that I am. Give me a chance please.”
“Am sorry. Allah Ya baka wadda ta fini.”
Kafin ya amsa ta katse kiran. He called back immediately amma har wayarta ta kashe. Ransa ya baci sosai. Amma a zuciyarsa he was thankful da Allah bai bashi damar yaudararta ba. Sake kiranta kuma wajibi ne don ita kadai yake ganin zai iya yiwa tambaya a kan Tahir ta bashi amsa ba tare da tayi zargin komai ba. He’ll just have to change his tactics. Yaudarar da yake gudu may come in handy.
Ana dara ga dare yayi.
We all know that Tahir is not the Saint he pretends to be.
Who is he?
Ooops! Join The Community To View The Comments