Polygamy In My Mind
Ƙarin aure, jimla mai kalma biyu sai uban kwarjini. Maza na ƙaunarta , mata na ƙyamarta. Da an furta ta sai kaga wata irin nutsuwa ta shigi mata. Abin babu babba, babu yarinya. Waɗanda za a aurowa so su ke su ji wai me wance tayi da za ayi mata kishiya. Ɓangaren wacce za a auro kuma suna son sanin da me ta gidan ta gaza ake son ɗaukowa daga family ɗin su.
Truth be told, polygamy will never have a consensual meaning a tsakanin mutane. Kowa fuskar da yake kallonsa daban, mun yarda it’s permissible. No Muslim dares to dispute the ruling. Amma fa idan har yinsa za ayi da gaske, kowa zai dauko lense daban ya kalle shi ta fuskar da yake so. And so, I call polygamy a multi-faceted institution. Everybody involved sees and interprets it from an entirely different angle that has their interests at heart.
Akwai mahangar miji da ta danginsa wadda babu lallai ta kasance akan turba ɗaya. Idan baka yi da gaske ba ma sai a kafa maka jam’iyyu na adadin matanka. Kowa ya bi wacce yake so. Idan ta kwabe a wata ma akwai damar canji.
Matar cikin gida ma da nata dangin have their own understanding. Almost every time miji zai ƙara aure sai an kira shi butulu kuma maci amana. A wurinsu kawai laifi kayi musu. Few times ake samun understanding amma fa deep down the pain is raw. Gani take za ka nemo wata saboda ka raina ƙoƙarinta ko ka daina sonta.
Amarya and her entourage kuwa believe that matar gidan ta gaza ne. Ko mijin ya faɗa ko bai taba faɗa mata ba su dai a wajensu tasu daidai take da Avatar…you know, that saviour that can and will do anything for the happiness they assume he lacks.
Ko ma dai mene ne, we are going to look although on the surface only to see some of the things that shape a polygamous home.
Yan aji, what do you fear most about polygamy?
Ooops! Join The Community To View The Comments