A Bond Broken 4
Four days have passed daga ranar da Hamdaan ya kira Inaya. Kuma a cikin kwanakin, not an hour goes by da tunanin muryarta baya dawo masa. He even saved her name as The Voice. Ranar da abin ya ishe shi, he sat down in his office and sent her an sms.
(Salam, it’s me again. Can I call you?)
Har lokacin tashi yayi babu reply. Yana aiki da Hisbiscus Bank as an Investment Analyst. A gefe kuwa he has his own thriving real estate practice wanda ya fara from the scratch. He started kafin ya fara aiki. Da aikin ya samu kuma sai ya nemi mataimaka. Su yi aiki cikin sati, shi kuma da weekends. Sosai yake building aikin real estate ɗin saboda yana sa ran ya bar bank nan gaba. Like his father, Hamdaan wants to stand on his feet. Shi yasa yanzu he is always busy. Hardly at home. Mami ta ma gaji da magana. Burinta yayi aure, hopefully ayi dace ya ragewa kansa aiki.
Ya gama tattara kayansa a bagpack ɗinsa ta office, yaji ba zai iya fita ba sai ya sake neman Inaya. Like seriously her voice is just too mesmerizing. And by God, he hates this new desperate version of himself.
‘Anya ba matsafa bane? Abin da ya rage tsakani na da obscession is just a thin line fa’ yayi cautioning kansa.
Contemplating between calling and texting her again for the last time yake yi abokinsa Suhail ya shigo office ɗin. Sam bai ji ba. Yayi nisa wajen tunani.
Kafaɗar Hamdaan yayi shaking gently
“Guy tunanin me kake yi ne?”
Hamdaan looked at him abruptly “The voice.”
“What? Are you trying to audition?” Suhail ya ƙyalƙyale da dariya sannan ya ce “Disaster.”
“Kai fa ɗan iska ne. Nayi maka kama da mawaƙi?” Hamdaan ya kai masa duka shi kuma ya goce.
Suhail ya cigaba da dariya “Na sani ko NYSC anthem za ka rera musu.”
Hamdaan ma dariyar yayi remembering their NYSC days. Akan waƙar nan yaci wahala. Aka raɗa masa suna Youth Obey. Corps members su faɗa, Officers ɗin dake kula dasu suma su faɗa. Dalili kuwa shine a irin wayar nan ta dare wata budurwarsa tace tana so yayi mata waƙar ta iya kafin lokacinsu in the next two years. Giyar soyayya ta bugar da samari, he started singing ba tare da tuna a ina yake ba. Ranar ɗakinsu anyi dariya kamar me. Muryar Hamdaan ɗin was hoarse, babu wani kari a cikinta. Suhail took a video wanda Hamdaan had to pay him da wanki da ɗiban ruwan wanka kafin ya goge.
“Mugu, har ƴaƴanka sai na faɗawa yadda ka ci amanata.”
“Soyayya dai taci amanarka. After all the singing yanzu tana ina?” Cewar Suhail har lokacin dariya bata bar shi ba.
Hamdaan shrugged “Wa ya sani ne? Maybe tayi aure.”
Ya buɗe motarsa. Suhail yana daga waje ya duƙo kansa.
“Akan ka na san gaskiya love is a scam. Ni auren dole ma zanyi kawai.”
Hamdaan ya kama buttons ɗin shirt ɗinsa na sama guda biyu yana buɗewa ya bashi amsa da cewa
“Ni dai I’ll keep getting scammed until I find the legit one.”
“Malam wahale I salute you. Yanzu dai kafin na gudu ka fasa ƙwan mana. Who is the Voice?”
“Gasar waƙa ce ka zo mu shiga tare.”
“Ina nan za ka zo ka bani labari. Sai na gama shan ƙamshi zan saurareka.”
Hamdaan ya girgiza kai. Mutane suna ganin he is too playful, basu san halin Suhail ba. Shi a tasa rayuwar kamar babu wani serious abu sama da cin abinci. Hannu ya ɗaga masa yaja mota. Shima Suhail ya shiga tasa motar ya tafi.
*
On reaching home, motar Hamida ya gani a parking space. Direban su kuma yana can tare da direban Mami suna hira a jikin mota. Da murnarsa ya shiga gidan. Amal da Hanan suka taso daga wajen Abba suka rungume shi.
“Kai ku bar min ɗan auta ya huta don Allah.”
“Kin ji fa Hamida.” Cewar Abba yana kallon Mami ta ɗauke Hanan daga jikin Hamdaan tace ya tafi yayi wanka “ƙaton tuzurun nan take kira ɗan auta.”
Hamida ta taɓe baki “Ai Abba baka ga komai ba. Nifa tun shigowata zancensa take yi min. Irin abin nan na an kwana biyu ba a ganni ba ma duk babu.”
“Wanda nake yi miki ma albarkacin kin rako ɗan auta duniya ne.” Mami ta ƙare maganar da dariya domin kuwa Hamida kamar za ta yi kuka.
Tsam Hamdaan ya tashi ya koma kusa da Hamida ya ɓata rai “Mami ya haka ne? Twinnie ce fa. Gidan nan kaf ɓacin ranta yafi damuna.”
“Harda ni uwa..ka?” Fuskar Mami a haɗe, Abba kuwa me zai yi banda dariya “to dai aljannarka a nan take.” Ta buga ƙafa a ƙasa.
“Taki kuma a nan ba.” Abba ma ya buga tasa ƙafar.
Mai aikinsu Lamisuwa sai dariya. Diramar gidansu bata ƙarewa. Sai dai idan basu haɗu ba. Ta dubi iyayen gidan nata.
“Ayi haƙuri Hajiya. Ayi haƙuri Alhaji. Ƴan biyu ayi haƙuri.”
Kowa kuma sai ya dara. Hamdaan ya wuce zai shiga ɗaki Hamida ta bishi. Mami har ta manta za ta hanata Abba ya dakatar da ita.
“Ƙyalesu mana. Tunda ta zo fa tace shi take nema.”
Hanan da Amal ta nuna masa “zugar ƴaƴanta binsa zasu yi a hana shi hutawa.”
“Arziƙi ne. Ki barsu.”
Dole ta kaɗa kai ta haƙura.
*
Gajiya da jiran me Hamida zata ce Hamdaan yayi ya kama ƙofar toilet.
“Kin san bana son jan rai Twinnie. Kin saka ni a gaba kin kuma ƙi yin magana. I realy need to take a shower kafin a kira Magrib.”
“Ba sai ka kore ni ba ai. Zan fita.”
She is angry he can tell. Abin da ya ɓata mata rai ne dai bai sani ba tunda lafiya ƙalau suka gama magana a gaban su Mami.
Kai tsaye ya ce “Me nayi miki?”
“Tunda ka san kayi ba daidai ba sai ka canki laifin ma.”
Shi da ita zani ce ta tarar da mu je mu. Idan suna cacar za ka rigimar tabbatar sakwanni is real.
“Am not ready to exchange words with you. Ki faɗa min ko ki fita.”
“Why?” She asked softly, pushing her anger aside.
“Why??” Ya tambayeta shi ma all confused.
“Twinnie ka bi Abban Amal har airport ko kuwa?”
“Ƙarya zan miki? Akan me?”
“To me yasa ka ƙi faɗa min ka ganshi yaje wani gida ya ɗauki mata har biyu?”
Sakin baki Hamdaan yayi.
“He told you?”
“Yes, because he is not the cheat you thought he is.” Ta riƙe ƙugu, her bump looking like an inflated balloon. Da sauri Hamdaan ya kawar da kansa don kada yayi mata dariya.
“When did I say that?”
“Idan ba haka ba to me yasa ka bar maganar? You didn’t do me a favour by the way. Shirun ka only meant you are fine na auri maƙaryaci.”
“I was trying to protect you. Yanzu imagine ace tun ranar na faɗa miki. Kina tunanin ko me zai faɗa miki za ki yarda?”
Ɗan tunani tayi ta girgiza kai “a’a, amma dai that does not give you the right…”
“Naji, Allah Ya baki haƙuri. I was wrong to assume bincike ya kamata na fara yi kafin na tayar miki da hankali.”
Jikinta sanyi yayi. Ta turo baki.
“Am sorry. I got all emotional wallahi.”
“Kin dai zo ki sauke min crazy pregnancy hormones ɗin ki.”
“Kai Twinnie” tayi murmushi.
“Ki dinga bin komai a hankali. Wannan dalilin ne yasa na ɓoye miki. Ina jira na tabbatar da abin da yake tsakaninsu.”
They sat down akan single cushion chair ɗin ɗakin. Hamdaan yayi mata bayanin komai game da numbar ƙanwar mai cikin da ya karɓa.
“Any progress?” Ta ɗage gira.
Hamdaan yayi gajeren tsaki “ina fa.”
And because they never kept secrets a tsakaninsu, ya sanar da ita yadda yake ji game da yarinyar.
“It’s not love, I know kafin ki ce min mahaukaci.” They laughed together, “I just want to know her.”
“Bani wayarka”
Ya miƙa mata. Ta buɗe saboda password ɗinsu har always been their birthday. Ya faɗa mata sunan da yayi saving numbar tayi murmushi. Whatsapp ta buɗe ta kalli profile pic ɗin Inaya.
“Kinga abin haushi ko.” Cewar Hamdaan sounding all hurt.
Ga dai hoton budurwa iya fuska. Amma ta sanya hannu ta rufe rabin fuskar from her eyes. Part of her nose zuwa haɓa ake iya gani. She has a chocolate complexion with a right side dimpled cheek and a beautiful smile.
Hamdaan bai ankara ba Hamida tayi tapping speaker ta fara recording voice note.
“Assalam alaikum. Hey Inaya, I am the twin. Ɗan uwana ya kawo min ƙarar ki. Kina so mu yi miki ƙofi ne?”
“Are we 16? What are you doing Twinnie?” ya miƙa hannu da sauri ita kuwa ta saki ya tafi.
“You dey craze.” Hamdaan ya faɗa gadonsa ya zauna da yaga abin da tayi.
“You too” Hamida ta harare shi.
Zai yi deleting kenan ya kula da alamun an saurara. Hankalinsa ya tashi. Kawai sai yaga Inaya is recording.
“Duba ki gani.”
Hamida ta dawo kusa dashi ta zauna. After few seconds voicenote yayi dropping. Da sauri Hamdaan yayi playing. And the voice hit him once again. She was laughing.
“Wa alaikum salam. Ina ƙanwarki za ki yi min ƙofi Anti.”
Hamida ta tura mata da amsa “Anti kuma? We are just 29. Gaskiya bana son tsufa.”
Inaya sent a laughing emoji.
Hamida smiled and recorded again “My bro is a nice guy. Bana so ki yi missing sanin mutum kamar shi.”
“Ni soyayya ce bana so.” Was Inaya’s reply in a sad tone.
Hamdaan felt it to his bones. Hamida looked at him as she was about to start recording. Irin abin nan na ƴan biyu, sai suka faɗi abu ɗaya a tare.
“I’ll be your friend”
“He can be your friend”
Inaya wrote (ba na abota da maza.)
Hamdaan karɓe wayarsa yayi daga hannun Hamida. Ya nuna mata ƙofa taƙi fita. Ya zare mata ido ita ma ta zaro masa nata.
“Suit yourself.” Ya ce sannan yayi recording with a reassuring voice.
“I’ll be that shoulder everybody needs in their down moments Inaya. Zan saurare ki. Zan kwantar miki da hankali. Zan kuma baki shawara. Please let me in.”
It took her about 5 mimutes kafin ta tayi replying. Gabaɗaya sun ƙosa da jira shi da Hamida.
In a cool voice, Inaya said “Thank you. Wai yaya sunan ka ne? Kai ne Hassan ko Hussain?”
Ya rubuta (Hussain)
(Nagode. Sai mun yi magana)
Shi da Hamida tafawa suka yi. Amma sai da ta tambaye shi dalilin ƙaryar suna. Yace mata baya son abin da zai koma kunnen Tahir har ya gano zargin da yake yi masa.
Zuwan Mami ne ya katse musu hirar.
“Dama nace ba za ki barshi ya shirya ba. Oya zo ki fita kada ki koyawa ɗana zama da tsamin jiki.”
“A taƙaice dai tsami ɗan naki yake yi”
Hamida ta fice tana dariya. Hamdaan kwanciya yayi yana ta playing vn ɗin. The voice is down today. Tana da damuwa ba ma sai ta faɗa ba. Damuwar har tayi tasirin da tasa ta canja ra’ayi ta saurare shi yau.
*
Inaya blicked her eyes furiously saboda kada tayi kuka. The fleeting distraction that came with hirar su da Hussain and his twin whose name she thinks is Hassana has left her. Abin da yake damunta ya dawo sabo fil. Yayyen mahaifinta sun gama maganar aurenta kamar wata ƴar tsana without her consent and her Mom is in full support.
Akwai ɗan wan mahaifinsu da yake aiki a Poland. Tun undergrad ya tafi har ya gama PhD bai sake zuwa Nigeria ba. Ya kama aiki yanzu 14 years rabon da kowa na gida ya saka shi a ido. He has been dating a Polish lady for five years. His Mum played the over-my-dead-body card akan auren. It was successful amma yaƙi dawowa. Shi ne aka yanke shawarar ayi masa auren gida a tura masa matar. And she Inaya, is the unlucky one to be chosen.
Dear Readers,
Say your thoughts in the comments section.
Ooops! Join The Community To View The Comments