To The Bride And Bestie
Ƙawance tun zamanin Aunty da Uncle na Nursery da Primary. A tafi Islamiyya tare a dawo ana gulmar Malam wane saboda yayi dukan hadda. Da kallo kawai kuna iya yin hira sai dai dariyar ku ta cika aji. Abin takaici ko bulala ake yi muku, you still manage to laugh as long as you are together. Rayuwa ce full of innocence, tun kuna kwailaye har kowacce ta dauki shape din kwalbar minerals.
Danginku duka sun san ku tare. You know each other’s crush and first love. Ku ne compaign officers din juna wajen zaben saurayi. Idan anyi fada ku shirya su. Yawon fitar da anko, gajiyar rabon kati da duk wani fadi tashin aure idan lokaci yayi you do it selflessly. Komai ke ake kira saboda kusancin ku har a kaita dakin mijin ta. Daga nan kuma sai ku kasa gane juna. You feel she is neglecting you, she feels you do not understand her. Friends become strangers.
Bestie, yanzu fa kawarki a karkashin ikon wani take. Addini ya fifita umarninsa akan na kowa. With that new status, there are odd hours that you should not expect her to talk or chat with you. Fita unguwa yanzu sai anyi mata izini, idan mai kulle ta aura iyayenta ma sai sun yi hakuri. Wahalar da ki ka sha da bikinta kuwa sai dai wata tayi miki. Not because she does not care. Aure nauyi ne dashi kuma rayuwar sirri ce da bai kamata ta fito miki da komai ba sai abin da ya dace.
Amarya change of status does not mean change of your circle. Keep your friends and treat them with kindness. Afterall, aure aka daura miki ba wulakanci ba. Whenever your friend needs you kuma situation ya sa you cannot be there for her, do not rub it in kina hura hanci ai ke aure gare ki. She is your friend, explain to her kindly without having to paint your spouse a villain. ‘Babu ruwanki da kawaye’ da iyaye ke fada lokacin aure ba yana nufin ki kori naki ba. It’s just an advice for you to know that there is a boundary you should not cross now da sunan kawance.
Please be understanding, treat each other with respect and your precious bond will only grow stronger.
Kina da kawar da ku ka rabu bayan daya daga cikin ku tayi aure? Me ya hada ku? Let’s learn from your experiences.
Ooops! Join The Community To View The Comments