Maza Mutanen Mu
You guys know we can’t live without you ko? Just like you can’t live without us.
But the problem is kuna jagawalgwala mana tunani. Eh mana, sai mu rasa batun wa za mu kama.
A karatun dai an ce mana ‘namiji ba dan goyo bane’ amma wani in ya zo shi sai ya goyaki yayi ta jijjige, wani kuma in ya lallaba kika goyashi sai kiga har beautifying bayan yayi saboda kirki da iya soyayya. Shi kuwa Mallam Wane mai kama da mutanen kirki yana zuwa zaki cafe shi ki goya, amma da ya sami waje sai ya gasa miki cizo. Ayi ayi ya sauko yaki saukowa, karshe sai an hada da taron dangi kafin a sauke miki shi.
A wani karatun kuma biya mana akayi aka ce ‘maza tabarmar ‘kaya’ ba za a nade ba kuma ba a isa a zauna a kai ba.
Ba wannan kadai ba; sai ace mana maza sun fi son mace kamila. Sai ki tattaro natsuwarki kin kame kanki sai ya rabu dake ya auri wata me rangwamen natsuwa. Ko kuma ya aureki amma ya koma yana bin watsattsu a waje.
Ga kyau, ga ilimin ga kuma tarbiyya amma sai a barta kama o’o.
Wasu lokutan muna rasa yanda zamuyi da ku fa; kwalliya, girki, tsaftar, nutsuwa duka mun hada amma ku rufe ido ku ki gani.
Ya ayyuhar-rijalu, take the mic and tell us what you want.
Matan aji ku gyara zama, let’s take some notes. Masu aure su sami na gyara aure, ‘yan mata kuma duk ku gyara a samu ayi wuf da ku.
Mazan aji come out and tell us the secret.
What is it that you want in a woman? What is that thing that a woman will do that will immediately sweep you off your feet? What should a woman do to get your attention and keep it?
Ooops! Join The Community To View The Comments