Bakin Amarya
Sati uku bayan biki amma har yanzu kusan kullum sai anyi baki. Yau ma batch biyu ne su ka tafi. Na tara gajiya sosai. After Asr, I went to the kitchen to do what I hate must cikin ayyukan gida, wanke-wanke. Ina cikin hada kwanukan a sink nayi bakuwa. I stood behind the closed gate and waited for her to introduce herself.
“Nafisa ce daga Yolawa”
Every guest from Yolawa is either from my husband’s family house or from one of his relatives. I let her in. Matashiya bata fi sixteen ko seventeen ba. She was all smiles calling me Aunty har mu ka shiga ciki.
“Aunty ina makaranta aka yi bikin ku. Boarding nake yi amma na kusa gamawa.”
Kara sakin jiki nayi da ita ina tambayarta mutanen gida. Daga nan na koma kitchen domin kawo mata abinci. Ina juyawa zan fita muka yi ido hudu. Cikina ya kulle saboda tsoratar da nayi domin ban ji motsinta ba. Ta kalli kitchen din ta shigo hankali kwance ta cigaba da harhada kwanukan da nake yi kafin zuwanta. She wouldn’t take no for an answer when she asked to wash the plates. Nima ban matsaba don na gaji da gaske.
I sat by the door akan karamar kujera. Nafisa tana aiki ta fara bani labarin makarantarsu. A SS2 take commercial class. Daga nan hirar ta koma ta masu aljanun makaranta. Horror iya horror naji a ranar. Ta kalli wani food warmer ta ce,
“Wani lokacin fa a kwanarmu idan aka tayar sai muce abincin gidan su wance zamu ci. Sai ki ga mai aljanun ta rufe ido. Bayan dan lokaci sai ta bude idonta ta leƙa ƙarkashin gado ta fito da flask kamar wannan…” she pointed at mine.
Jikina ya gama sanyi nace “abinci ne a ciki?”
“Na gidan su wadda aka ce ana so ba. Kwanon ma nasu ne.”
A yadda nake a tsorace da wani zai ce kyat, zan fyalla a guje ne zuwa inda kafata zata kai ni. Tun ina zaune sai gani tsaye a jikin kofar kitchen din.
“Kema ana dauko naku abincin kenan?”
She gave me a smile as if she was taunting me before answering “ni bani da komai.”
Nayi zaton zancen ya kare ashe da saura. This girl started telling me about irin gamon da ake yi a toilet da cikin rijiya idan sun je diban ruwa da yamma.
“wani lokacin ma kina kwance za ki ji kamar ana ja miki yatsun kafa ko ture ki kadan wata ta kwanta.”
Innalilllahi wa inna ilaihi raji’un. Daga ni sai Nafisan nan a gida. I was pretending to be brave amma na kasa daurewa. Ni da ko a makaranta bana zuwa kallon masu aljanu, yau ga abu har gida. I started reciting Ayatul Kursiyyu in my heart sannan nace mata ina zuwa, na tafi daki. I called my husband na tambaye shi wace ce Nafisan Yolawa. Yallabai sai cewa yai bai sani ba.
“Ban gane ba. Ta ce anyi biki tana school.”
“Kema dai Baby mutum nawa ne aka yi bikin suna school? Amma kin tambayeta ko ita yar waye a Yolawan?”
Daina fahimtar komai nayi saboda tashin hankalin da tambayar tasa ta sake jefani. I didn’t know when I started crying. Na fada masa irin hirar da take yi min. He asked me to hang up while he calls his sister. Kirana ya sake yi ya ce wai ita ma bata santa ba.
“Zauna a daki gani nan zuwa.”
As I sat down shaking, he called again and confirmed cewa ya tuna ko yar waye. Her Dad was their cousin. Nafi suke kiranta. Relief washed over me like cold water. I still waited in my room har ya dawo. This is one story I’ll never forget in my life. The fear was real. He saw it in my eyes because he gave me a hug and says “it’s okay.”
Bayin Allah da ku ne Nafisa ta zo gidan ku yaya za ku yi?
Ooops! Join The Community To View The Comments